Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A daidai lokacin gabatowar zagayowar ranar tunawa da harin ta'addancin da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai wa al’ummar kasar Labanon, jaridar Al-Akhbar ta rubuta a cikin wani rahotonta cewa: "Ta'afaina" wato "Mun Samu Lafiya" wanda shine taken da kungiyar Hizbullah ta zaba a cikar shekarar farko na kisan kiyashin na pager, amma wannan take ba wai kawai taken siyasa ba ne, sai dai yana nuni da irin gagarumin kokarin da cibiyoyin Al’umma su kai ga wadanda abun ya shafa na ba su kulawar lafiya bayan kawo karshen ayyukan gaggawa.
A cikin watan Satumban 2024, sojojin Isra'ila sun fasa na'urorin pager a yankunan fararen hula na Lebanon, lamarin da ya haifar da zubar jini da firgici. Bisa kididdigar da aka yi a hukumance, an kashe akalla mutane 20 tare da jikkata wasu fiye da 3,000. Yawancin wadanda suka jikkata sun samu nakasa ko makanta, inda mutane kusan 300 da suka hada da mata 11 da kananan yara 7 suka rasa idanunsu gaba daya.
Likitocin da ke wurin sun bayyana lamarin a matsayin wani kisan kiyashi da ba a taba ganin irinsa ba wanda ba yaki ba ne, sai dai kisan gilla ne da nufin gurgunta al’umma baki daya, kuma hotunan wadanda abin ya shafa, da fuskokinsu suka kone, da wadanda aka yankewa gabobinsu, da wadanda suka makance, har yanzu suna nan a fili cikin tunanin jama’a baki daya.
Gudanar Da Tallafin Gaggawa Da Janyewar Gwamnatin Labanon Kan Lamarin
A kwanakin farko, asibitocin gwamnati da na masu zaman kansu sun yi ɗaruruwan tiyatar gaggawa tare da jan hankalin jama'a. Ma'aikatar lafiya ta kasar Labanon, tare da kungiyar likitocin, sun kaddamar da wani shiri na neman magani na dogon lokaci, kuma an bude cibiyoyi na musamman a asibitocin Rafik Hariri da Baabda, amma wadannan yunƙurin ba su daɗe ba, kuma tare da rage farashin tsadar magungunan da ake bukata da gwamnati ta yi a kasa da rabin ainihin farashin, asibitoci da yawa sun ƙi karbar wadanda suka jikkata.
Sannu a hankali, bin diddigin hukuma ya dusashe kuma babban nauyin jiyya da kulawa marasa lafiyar ya faɗa kan wuyan cibiyoyin da ke da alaƙa da Hizbullah, ciki har da "Cibiyar Masu Rauni" da "Kungiyar Lafiya ta Musulunci." Baya ga ba da sabis na kiwon lafiya, waɗannan cibiyoyi sun kai ɗaruruwan da suka jikkata zuwa Iran, Iraki, da Siriya don ƙarin kulawar jiyya.
Tabarbarewar Tsarin Kiwon Lafiya
A cewar Dr. Abu Seth, wani likitan tiyata kuma sananne ne a fannin kula da wadanda yakin ya rutsa da su, babbar matsalar Lebanon ita ce tushen tsarin kiwon lafiya, wanda bai dace da yanayin yaki da manyan bala'o'i ba. Gwamnati tana bada kulawa ga marasa lafiya sai a lokacin gaggawa ne kawai, daga nan kuwa sai ta sallami maras lafiyar.
Dr. Elias Jaradi, likitan tiyatar ido kuma dan majalisar dokokin kasar Lebanon, ya kuma jaddada cewa da yawa daga cikin wadanda suka jikkata na ci gaba da rayuwa karkashin kulawar lafiya bayan shekara guda kuma domin samun saukinsu suna bukatar dogon lokaci.
Bisa kididdigar da likitocin suka yi, kowane daya daga cikin wadanda suka jikkata zai bukaci a yi manyan tiyata tsakanin biyar zuwa 12. Raunin ido ya haifar da mafi yawan damuwa; hatta wadanda basu rasa ido daya ko biyu ba suna cikin hadarin kamuwa da ciwon ido.
Cibiyoyi A Madadin Gwamnati
Tare da janyewar gwamnati, cibiyoyin Hizbullah sun dauki nauyin kulawa da su. Baya ga tallafin likitanci, Cibiyar Masu Rauni ta ƙaddamar da shirye-shiryen farfadowa na tunani da zamantakewar al'umma kuma ta mayar da hankali ga maido da 'yancin kai ga wadanda suka ji rauni ta hanyar ilimin motsa jiki, aikin motsa jiki, da kuma samar da gaɓoɓin wucin gadi. Cibiyar ta kuma shirya kaddamar da aikin tiyata na gyaran fuska musamman na gabobi.
Ita ma Iran ta taka rawar gani a fagen kasa da kasa. Rahotanni sun ce an kai mutane 445 da suka jikkata zuwa Iran tare da masu rakiyarsu a lokuta da dama, yayin da wasu kuma aka tura su kasashen Iraki da Siriya.
Duk da kokarin kungiyoyi masu zaman kansu, yawancin wadanda suka jikkata na ci gaba da kokawa da matsalolin kudi da na likitanci. A wasu lokuta, an tilasta wa iyalai su ɗauki nauyin jiyyar da kansu ko kuma su bar tafiya don ci gaba da jiyya. A wajen masu sa ido, gwamnatin Lebanon a zahiri ta ki cika ayyukanta na kasa ta hanyar "dora alhaki ga yanayin zamantakewar wadanda abin ya shafa".
Yanzu, shekara guda bayan waki’ar, wadanda Pager ya shafa har yanzu suna kan layi don neman magani da kuma tiyata; amma babbar tambaya da ta kasance ba a iya amsata ba: Shin gwamnatin Lebanon za ta karbi alhakinta ga 'yan kasar ko kuwa komai zai sake fadawa kan kafadun cibiyoyi masu alaka da juna da taimakon kasashen waje?
...................................
Your Comment